logo

HAUSA

Hadarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 28 a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya

2021-05-10 10:29:01 CRI

Hadarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 28 a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya_fororder_210510-kogin Niger

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar a kalla mutane 28, kana wasu mutane bakwai kuma suka bace, bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a wani kogi a karamar hukumar Shiroro dake jihar Niger a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Da yake karin haske kan lamarin, babban darektan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger (SEMA) Ahmed Inga, ya bayyana cewa, hadarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar agogon wurin, lokacin da wani kwale-kwalen katako dauke da mutane 100 ya daki wani kututturen bishiya kana ya dare a cikin kogin, ya kuma nitse a nisan kimanin mita 50 daga inda ya nufa.

Ya ce, ya zuwa yanzu dai, an kai ga ceto mutane 65, yayin da masu linkaya suka yi nasarar gano gawawwakin mutane 28, ana kuma ci gaba da neman mutane 7 da suka bace. Inga ya ce, ana ci gaba da aikin ceto, don gano raguwar mutanen da suka bace. (Ibrahim Yaya)