logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da shigar da Taiwan a babban taron WHO

2021-05-10 21:20:25 cri

Dangane da kalaman sakataren harkokin wajen kasar Amurka Anthony Blinken, na nuna goyon baya ga "shigar da yankin Taiwan cikin Majalisar Kiwon Lafiya ta Duniya", mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, sanarwa mai nasaba da hakan ta sabawa manufar Sin daya tak a duniya, da kuma tanadin dake cikin hadaddiyar sanarwa guda uku a tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, don haka, kasar Sin ta nuna matukar rashin gamsuwa, da adawa game da hakan.

Hua Chunying ta kara jaddada cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya. Kaza lika dole ne shigar da yankin Taiwan cikin kungiyoyin kasa da kasa, gami da ayyukan WHO, ya bi manufar Sin daya tak a duniya. Wannan ce kuma babbar manufa ta kudurin MDD mai lamba 2,758, da na babban taron WHO mai lamba 25.1, wadda ta samu goyon baya daga kasashen duniya.  (Bilkisu)