logo

HAUSA

Ragowar sassan rokar harba tauraron dan adam ta Long March na kasar Sin ya sake shiga sararin sama galibinsa ya kone

2021-05-09 17:40:57 CRI

Sashen karshe na rokar dake daukar tauraron dan adam ta kasar Sin ta Long March-5B Y2, ta sake shiga sararin samaniya da misalin karfe 10:24 na safe agogon Beijing, hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin, (CMSA) ta sanar da hakan.

Mafi yawan jikin na’urar ta kone a lokacin da take kokarin sake shigar, kana ragowar bangarenta ya fada cikin teku a nisan maki 2.65 daga shiyyar arewaci, kana da nisan maki 72.47 daga kusurwar gabashi, a cewar hukumar ta CMSA.

Na’urar rokar ta Long March-5B Y2, ita ce ke daukar tauraron dan adam na Tianhe, karon farko kuma muhimmin rukuni na aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, wanda aka harba tun a ranar 29 ga watan Afrilu daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Wenchang dake gabar tekun kudancin tsibirin lardin Hainan.(Ahmad)