logo

HAUSA

Sin ta yi nasarar harba sabbin rukunin taurarin dan Adam

2021-05-07 12:55:31 CRI

Da karfe 2:11 na safiya yau Juma’a ne, kasar Sin ta yi nasarar harba rukunin sabbin taurarin dan adam na kula da taswira, daga tashar Xichang dake lardin Sichuan, a kudu maso yammacin kasar Sin.

An harba rukunin taurarin ne ta amfani da rokar Long March-2C. Ana kuma sa ran yin amfani da su, wajen gano maganadisun lantarki mai nasaba da muhalli, da kuma karin wasu binciken fasaha.

Kaza lika an harba wannan rukuni na taurarin dan adam tare da wani tauraron, na rukunin taurarin Tianqi. Wannan tauraro mai suna Tianqi-12, zai yi aikin tattara bayanai ne, da kuma gabatar da su.

Wannan ne karo na 369 da ake amfani da rokar Long March wajen gudanar da irin wannan aiki a kasar Sin.  (Saminu)