logo

HAUSA

Sin:Zaman da majalisar wakilan Amurka ta kira game da batun Xinjiang adawa ce da kasar Sin

2021-05-07 19:47:08 CRI

Sin:Zaman da majalisar wakilan Amurka ta kira game da batun Xinjiang adawa ce da kasar Sin_fororder_汪文斌-1

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai da aka saba shiryawa Jumma’ar nan cewa, kwamitin harkokin wajen majalisar wakilan Amurka, ya gudanar da wani zama game da batun wai “kisan kare dangi kan ‘yan kabilar Uygur da sauran kananan kabilu a Xinjiang” ba tare da gabatar da shaidu ba.

Wang Wenbin ya kuma bukaci bangaren Japan, da ya kula da matsalar zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliyar Fukushima, ya kuma bari kasashen duniya su sanya ido.(Ibrahim)