logo

HAUSA

Kasar Sin ba za ta amince da duk wani yunkurin hargitsa Xinjiang ba

2021-05-07 15:24:50 CRI

Jakadan Kasar Sin a Amurka, Cui Tiankai, ya ce kasar Sin ba zata nade hannu ta na kallon wani yunkuri daga wajen kasar ya hargitsa yanayin jihar Xinjiang ko ma raba kasar ko kawo tsaiko ga bunkasarta ba.

Yayin wani taro mai taken “ Xinjiang yanki ne mai ban sha’awa” da aka yi ta kafar intanet wanda ofishin jakadancin da gwamnatin Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin suka shirya, Cui Tiankai, ya ce al’amuran Xinjiang, al’amura ne na cikin gidan Sin, kuma Sinawa biliyan 1.4 daga kabilu daban-daban ba za su kyale duk wani yunkuri na dakile ci gaban kasar ba

Ya ce, ana ci gaba da yayata karairayi game da Xinjiang da shafawa Sin bakin fenti da kuma kakaba mata takunkumai a Amurka da sauran kasashen yamma. Yana mai cewa, amma kuma karya fure take, bata ‘ya’ya.

Bugu da kari, ya ce abun da ake kira da kisan kiyashi, karya ce tsagwaronta, yana mai bada misali da alkaluman yawan al’ummar Uygur ta Xinjiang, wadanda suka ninka daga miliyan 5.55 zuwa sama da miliyan 12 cikin sama da shekaru 40 da suka shude.