logo

HAUSA

Sin za ta daidaita samar da hatsi da tabbatar da wadatar abinci

2021-05-07 12:56:00 CRI

Kasar Sin na daukar karin matakan daidaita samar da hatsi, da tabbatar da wadatar abinci, kari kan nasarorin da ta cimma a shekarun baya bayan nan, a fannin samun yabanya mai yalwa.

An bayyana hakan ne, yayin taron majalissar gudanarwar kasar da ya gudana a jiya Alhamis, karkashin jagorancin firaministan kasar Li Keqiang.

A jawabin sa yayin taron, firaminista Li ya ce, samar da daidaito a fannin noman hatsi, da kwazo wajen wanzar da noma isasshen abinci, sun kafa wani ginshiki mai karfi, na ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, sun kuma taimakawa yakin da kasar ke yi da annobar COVID-19.

Mahalarta taron sun yi amannar cewa, Sin na cin gajiya daga amfanin gona da aka fi bukata mai tarin yawa, wanda ake samarwa duk shekara, yayin da kuma ake kara azamar tabbatar da wadatar nau’o’in hatsi.

Taron ya amince cewa, yanzu haka an shiryawa tinkarar ayyukan noma na badi. Kana Alkamar da ake nomawa lokacin hunturu ta karu a karon farko cikin kusan shekaru 4, yayin da yanayin yabanyar ‘ya’yan itatuwa ya kara kyautata sama da na shekarun baya.

A daya bangaren kuma, ana hasashen samun karin yabanyar nau’o’in amfanin gona da ake nomawa lokacin zafi na bana. Yayin da tuni manoma suka fara ayyukan huda da shuka, na lokacin bazara yadda ya kamata, kuma an samu daidaito na fadin filayen noma da ake amfani da su wajen noma shinkafa.

Taron ya bayyana cewa, za a fadada filayen noman hatsi a duk tsawon shekara, kamar yadda za a yi hakan ga fannin noma masara.

A bana, an yi hasashen adadin hatsi da Sin za ta noma, ba zai gaza kilogiram biliyan 650 ba. (Saminu)