logo

HAUSA

Xi ya zanta da takwaransa na Saliyo ta wayar tarho

2021-05-07 20:00:08 CRI

Xi ya zanta da takwaransa na Saliyo ta wayar tarho_fororder_习近平-1

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Saliyo Julius Maada Bio ta wayar tarho.

Yayin zantawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a shirya kasarsa ta ke ta karfafa hadin gwiwa da Saliyo a yaki da annobar cOVID-19, za kuma ta baiwa Saliyo taimako da goyon bayan a yakin da ta ke yi da wannan annoba.

A nasa jawabin shugaba Bio ya bayyana cewa, a shirye kasar Saliyo ta ke ta zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu, da karfafa alaka da Sin a fannonin ilimi, da lafiya, da samar da abinci.

A wannan rana kuma, shugaba Xi ya zanta da takwaransa na Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) Felix Tshisekedi da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomaa Bach.(Ibrahim)