logo

HAUSA

Bai kamata kananan yara su rika kalllon fuskar na'urorin laturoni tsawon fiye da awa 1 a ko wace rana ba

2021-04-30 19:09:28 CRI

Bai kamata kananan yara su rika kalllon fuskar na'urorin laturoni tsawon fiye da awa 1 a ko wace rana ba_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20181017_a0158fd7fa8443ff8ae9ba502f445588.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Wata sabuwar shawarar hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta yi bayanin cewa, bai kamata kananan yara da shekarunsu ba su kai 5 da haihuwa ba, su rika kallon fuskar na'urorin laturoni tsawon fiye da awa 1 a ko wace rana ba, kana kuma ya fi kyau a hana jariran da shekarunsu ba su kai 1 a duniya ba kallon fuskar na'aurorin laturoni baki daya.

Wannan shi ne karo na farko da WHO ta ba da bayanai dangane da kiwon lafiyar kanan yaran da shekarunsu ba su kai 5 a duniya ba, inda ta bukaci kananan yara su rika motsa jiki, da samun isasshen barci. Haka kuma, ta tunatar da iyaye da su kare kananan yara daga amfani da telibijin da kwamfuta fiye da yadda suke bukata.

WHO ta yi bayani da cewa, ya kamata a tabbatar da kananan yaran da shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 4 a duniya ba suna motsa jiki ta hanyoyi daban daban fiye da awoyi 3 a ko wace rana, yayin da jariran da shekarunsu ba su kai 1 a duniya ba, a rika motsa musu jiki sau da dama a ko wace rana, musamman ma wasa dasu zaune a kasa, tare da hana su taba na'urorin laturoni duka.

A cewar WHO, zama kan kujera na dogon lokaci, rashin isasshen motsa jiki, muhimman dalilai ne dake haddasa karuwar yawan mutane wadanda nauyinsu ya wuce misali a duniya. Yanzu baliban da yawansu ya kai kaso 23 da matasan da yawansu ya wuce kaso 80 a duniya ba sa motsa jiki isasshe. Haka kuma yawan kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 wadanda nauyinsu ya wuce misali ya kai miliyan 40, adadin da ya kai kaso 5.9 bisa jimillar kananan yara a duk duniya baki daya. Yadda nauyin mutane ya wuce misali, ya kan haddasa kamuwa da ciwon magudanar jini a zuciya, ciwon sukari, hawan jini da ciwon sankara.

Rashin isasshen barci cikin dogon lokaci, wani muhimmin dalili ne na daban da ya sa nauyin mutane ya wuce misali. A ganin WHO, kananan yara masu yawa suna daukar tsawon lokaci suna kallon telibijin ko kuma amfani da na’urorin laturoni, don haka ba su samun isasshen lokacin barci. WHO ta yi nuni da cewa, wajibi ne a tabbatar da jariran da shekarunsu ba su kai 1 a duniya ba sun dauki awoyi 12 zuwa 16 suna barci a ko wace rana, sa’an nan wadanda shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 2 a duniya ba su dauki awoyi 11 zuwa 14 suna barci a ko wace rana, kana ‘yan shekaru 3 zuwa 4 su dauki awoyi 10 zuwa 13 suna barci a ko wace rana.

Kananan yara kan samu saurin girman jiki da kuma karuwar kwarewar fahimta. Idan sun rika motsa jiki, da yin barci isasshe, to, zai taimaka wajen samun salon zaman rayuwa mai nagarta a nan gaba, tare da kare su daga kamuwa da matsalar kiba da sauran cututtuka. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan