logo

HAUSA

Lawal Saleh: Jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ita ce babban dalilin ci gaban kasar

2021-04-30 15:58:59 CRI

Lawal Saleh: Jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ita ce babban dalilin ci gaban kasar_fororder_微信图片_20210430155642

Lawal Saleh, wani mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum, kana masanin harkokin kasashen waje dake birnin Abuja na tarayyar Najeriya. A zantawarsa da Murtala Zhang, Lawal Saleh ya bayyana ra’ayinsa kan jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin.

Bana ne jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke cika shekaru 100 da kafuwa. Lawal Saleh ya waiwayi tarihin jam’iyyar, tun kafuwar ta a shekara ta 1921, har zuwa yanzu, wato yadda jam’iyyar kwaminis ta jagoranci al’ummar kasar Sin a gwagwarmayar kwato ‘yanci, da raya kasa da sauransu.

A cewar malam Lawal, a karkashin jam’iyyar kwaminis, musamman jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta samu tarin nasarori a fannoni da dama a wadannan shekaru, al’amarin da ya sa kasar ta samu babban ci gaba a fannoni daban-daban.

Lawal Saleh ya kuma bayyana kyakkyawan fatansa ga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kuma yadda za’a inganta mu’amala da dangantaka tsakanin kasashen duniya musamman kasashen Afirka karkashin wannan jam’iyya. (Murtala Zhang)