logo

HAUSA

Wane ne jigon tawagar kwallon kafar mata ta Steel Roses

2021-04-29 15:42:20 CRI

Koci Jia Xiuquan na tsaye kusa da ragar kungiyarsa, yana jan nunfashi sannu sannu, yana jiran a busa usur na karshe, kuma nan take da busawar, hawaye suka zubo daga idanun sa, yayin da ‘yan kallo sama da 13,500 suka mike tsaye suna Shewa da tafin murnar samun nasara.

Koci Jia mai shekaru 58 a duniya, da tawagar ‘yan wasan kwallon kafar mata ta Sin, wadda ake yiwa lakabi da Steel Roses, sun yi nasarar samun gurbin buga gasar Olympics wadda birnin Tokyo zai karbi bakunci, bayan tashi wasa 2-2 da koriya ta kudu, a zagaye na 2 na wasannin neman gurbin buga gasar, wadda kasashen nahiyar Asiya ke bugawa. Kungiyoyin biyu dai sun kammala wasan na karshe na neman gurbi a birnin Suzhou na nan kasar Sin.

Da yake zantawa da manema labarai, Koci Jia ya ce "Ku yi hakuri! Mun sa ku jin dar dar. Wannan wasa ya ba mu wahala fiye da abun da muka yi tsammani”. Ina son godewa ‘yan wasan mu, saboda ba su karaya ba. Muddin mun ci gaba da kwazo, na yi imanin kungiyar mu za ta ci gaba da cimma nasara da kwarewa".

A yayin wasan neman gurbin, ‘yar wasa Wang Shuang ta taka rawar gani, inda ya ciwa kasar Sin kwallo daya, ta kuma taimaka wajen cin wata kwallon, kuma kafin hakan abokan wasan su koriya ta kudu, na gaba da kwallaye 2 da suka ci a farkon wasan.

Ba bu batun karaya

Daga karshe koci Jia ya samu damar yin bacci mai kyau, bayan tsawon lokaci shi da ‘yan wasan sa na fafutukar neman gurbin buga gasar Olympics, ko da yake a lokacin da yake tsokaci game da wasan, jikin sa na amsawa saboda tunanin halin da suka shiga, kafin kaiwa ga nasara.

Ya ce "Na fara zaton ba za mu yi nasara ba, da hakan ta faru da na dauki alhakin rashin nasarar mu," wato yana batun lokacin da Sin ke bayan koriya ka kudu da ci 2 da nema, kafin “reshe ya juye da mujiya”.

Duk da wannan yanayi, a lokacin hutun rabin lokaci, Jia ya nufi wurin da ‘yan wasan sa suke sauya kaya, ya kuma ja hankalin su da kar su karaya, su fuskanci wasan da karfin zuciya. Ya ce "Ina son sake duba dabarar mu, abu mafi muhimmanci ma, ina son ganin yadda zan karfafa gwiwar su yayin da suke cikin wannan babban matsi.

Ya ce "Ba za mu karaya ba! Har abada. Muddin akwai sauran lokaci, to muna da dama!" Tamkar muryar Jia na ci gaba da maimaituwa a dakin hutawar ‘yan wasa. Bayan dawowa hutun rabin lokaci, sai Jia ya gudanar da sauye sauye da dama, kuma daga karshe sauyin ya haifar da nasara

Yang Man ta taso daga benci, ta kuma haifar da sauyi a wasan. Mai tsayin mita 1.86, tana kuma buga tsakiyar gaba, ta ci gaba da sarrafa kwallo, har ta kai ga saka kwallon da Wang ta bugo da kai cikin ragar abokan karawa, a minti na 68, wanda hakan ya sanya aka tafi karin lokaci, bayan kammala buga mintuna 90.

Jia ya ce "A wannan lokaci ba abun da ya rage mana sai rike wasa har karshen lokaci. ‘Yan wasa na sun hade kai wajen tabbatar da hakan, sun jure matsi sosai. Na yi matukar alfahari da kwazon su a filin wasa, musamman yanda suka rike wasan da ya kai har sa’oi 2."

Makomar Steel Roses

Game da matsayin kungiyar kwallon kafar mata ta Sin, koci jia ya ce, yanzu haka Sin na matsayi na 15 a duniya, inda ta ke gaban koriya ta kudu da maki 3. Amma fa tazarar gurbi 3 ba ta da yawa sosai.

Ya ce annobar COVID-19 ta haifar da cikas ga shirin buga gasar Tokyo, kuma halartar gasar daga ko wace kasa, zai zama wani mataki na gwada karfin kasashen game da yaki da cutar. Jai ya ce "Ba bu banbanci mai yawa tsakanin matakan yaki da COVID-19 a Sin da koriya ta kudu. Kare rayukan mutane ne shi ne kan gaba a duk kasashen biyu".

Ya ce "An dage wasannin da muka buga da lokaci mai tsawo, amma dukkanin mu mun yi karfin hali da burin samun nasara. Ya ce "Na shiga gasar Olympics ta shekarar 1988 a matsayin dan wasa. Na kuma yi burin shiga gasa dake tafe a matsayin mai horaswa, tare da ‘yan wasa na".

Jai ya kara da cewa "Zan so a ce akwai karin ‘yan kallo, da ‘yan wasan kwallon kafa, da karin ‘yan jarida masu karfafa gwiwar ‘yan wasan mu mata, ko da suna cikin filin wasan suna kallo, ko suna waje.

Game da batun gasar Olympics din dake tafe kuwa, Jia yana da karfin gwiwa. Inda ya ce "Duk wani mataki da aka aiwatar ci gaba ne, kuma burin mu shi ne mu kara gogewa ".

Kuma a yanzu, Jia na da karfin gwiwar ganin ‘yan wasan sa sun rike tagomashin su, wanda tuni ya karfafi gwiwar miliyoyin al’ummar Sinawa.