logo

HAUSA

Musa Garba Fari: Ya dace matasan Najeriya su sanya buri tare da kokarin cika shi

2021-04-27 14:02:50 CRI

Musa Garba Fari: Ya dace matasan Najeriya su sanya buri tare da kokarin cika shi_fororder_微信图片_20210422210152

Musa Garba Fari, dan Najeriya ne dake karatu a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. Malam Musa, wanda ya shafe kusan shekaru biyar yana karatu a China, ya yi bayani kan yadda yanayin karatu yake a kasar, da yadda yake mu’amala da mutanen China, inda a cewarsa, mutanen China mutane ne masu kirki da nuna karamci ga baki ‘yan kasashen waje.

Game da batun watan azumin Ramadan mai girma, malam Musa ya ce ya ji dadin rayuwa da gudanar da harkokin ibada yadda ya kamata a kasar Sin, kuma a nasa ra’ayin, bai yarda da jita-jitar dake cewa wai China ta hana musulmi yin azumi ba.

Bugu da kari, malam Musa, wanda ke dab da kammala karatunsa na digiri na farko a fannin gine-gine a Shenyang, ya yi kira ga mutanen Najeriya, musamman matasa, su tashi tsaye su yi aiki tukuru, don neman cimma burin da suka sanya a gaba. A cewarsa, idan sun yi nasarar cimma burinsu, za su iya kara taimakawa sauran mutane. (Murtala Zhang)