logo

HAUSA

Takardun bayanai na Australia sun fallasa kulle kullen wasu kasashen yamma na haifar da hargitsi a Xinjiang

2021-04-15 21:15:54 CRI

Takardun bayanai na Australia sun fallasa kulle kullen wasu kasashen yamma na haifar da hargitsi a Xinjiang_fororder_15

A baya bayan nan, wata kafar wallafa bayanai dake kasar Australia, mai suna "Australian Alert Service", ta wallafa wasu rahotanni 8 a jere, wadanda suka yi cikakken bayani game da kulle kullen da Amurka, da wasu kasashen yammacin Turai ke yi, na tallafawa ‘yan aware, da ayyukan ta’addanci a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba shiryawa, a yau Alhamis, ya ce duk rintsi gaskiya sai ta bayyana, kuma yunkurin Amurka da wasu kasashen yammacin duniya, na dakile zaman karko da ci gaban jihar Xinjiang ta kasar Sin, ba zai yi nasara ba.

Zhao ya kara da cewa, aniyar Amurka ta janye sojojin ta daga Afghanistan, na da nasaba da abun da Amurkar ke kira da "Matakin tunkarar kalubalen Sin", wanda hakan ka iya kara gurgunta amincin dake tsakanin Sin da Amurka.  (Saminu)