logo

HAUSA

Jarin Sin na ingiza ajandojin sauye sauye a Afirka, in ji wasu kwararru

2021-04-15 20:39:36 CRI

Jarin Sin na ingiza ajandojin sauye sauye a Afirka, in ji wasu kwararru_fororder_中非-1

Wasu kwararru da suka halarci taron karawa juna sani, game da harkokin kasuwanci, wanda cibiyar nazarin harkokin kasuwanci ta Sin ko CBSI, da hadin gwiwar jami’ar birnin San Francisco na Amurka suka shirya, sun ce ya kamata kasashen nahiyar Afirka, su yi amfani da damar zuba jari da suka samu daga kasar Sin, wajen kawo sauyi na gari, ga fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’ummun su.

Kwararrun wadanda suka halarci taron ta kafar yanar gizo a yau Alhamis, sun ce tarin jarin kudade da kasar Sin ke shigarwa sassan nahiyar Afirka, na gaggauta damar nahiyar ta cimma nasarar ajandojin sauye sauyen ta, da ma batun farfadowar ta daga cutar COVID-19.

Sama da mutane 200 ne suka halarci taron, ciki har da masu tsara manufofi, da shaihunnan malamai, da kwararru a fannonin samar da ci gaba.

Taken taron shi ne "Nazari game da jarin da Sin ke zubawa a nahiyar Afirka: alkawura da tasirin hakan ".  (Saminu)