logo

HAUSA

Farfadowar tattalin arzikin Sin ta taimaka ga farfadowar sauran yankunan duniya

2021-04-15 15:09:49 CRI

Farfadowar tattalin arzikin Sin ta taimaka ga farfadowar sauran yankunan duniya_fororder_tattalin arziki

A kwanakin baya ne babbar direktar asusun bada lamuni na duniya wato IMF Kristalina Georgieva ta tattauna ta kafar bidiyo da ’yan jaridar kamfanin dillancin labaru na Xinhua, inda ta bayyana cewa, a halin yanzu tattalin arzikin Sin ya farfado yadda ya kamata, matakin da ya taimaka ga farfadowar sauran yankunan duniya. Ta yi imanin cewa, ya kamata kasashen duniya su yi amfani da damar tinkarar cutar COVID-19 da sauyin yanayi, da kara zuba jari da yin hadin gwiwa ba tare da gurbata muhalli ba, da sa kaimi ga samun farfadowar tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli da yin la’akari da bambance-bambance ba. Sin ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

Georgieva ta bayyana cewa, sabon rahoton da IMF din ya fitar, ya daga hasashen da ya yi game da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, daga kashi 8.1 cikin dari zuwa kashi 8.4 cikin dari. Tana kuma fatan kasar Sin za ta ci gaba da kara samar da daidaiton tattalin arziki, ta hanyar ingantawa da kyautata tsarin bada tabbaci ga al’umma, ta yadda za a kara kashe kudi. (Zainab)