logo

HAUSA

Jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Nijeriya

2021-04-15 10:50:54 CRI

Jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Nijeriya_fororder_0415-01

A jiya ne, jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya gana da ministan kiwon lafiya na kasar Nijeriya Osagie Ehanire.

A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya, kasashen biyu sun raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata. Bana shekara ce mai muhimmanci, Sin tana son ta waiwayi tarihin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tare da Nijeriya, da hangen makomarsu, da yin amfani da rawar kwamitin kula da harkokin gwamnatocin kasashen biyu wajen bada jagoranci, da sa kaimi ga raya dangantakar kasashen biyu, da kara yin mu’amalar fasahohin tafiyar da harkokin kasashen biyu, da kara yin mu’amala a tsakanin manyan jami’ai gami da al’ummomin kasashen biyu, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin kiwon lafiya kamar allurar rigakafin cutar COVID-19, ta yadda hakan zai amfanawa jama’ar kasashen biyu.

A nasa bangare, Osagie Ehanire ya bayyana cewa, Nijeriya da Sin sun dade suna sada zumunta da juna, Sin ta taimakawa kasar Nijeriya wajen gina kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyin motoci, da asibitoci da sauransu, musamman bayan abkuwar yaduwar cutar COVID-19, Sin tana daya daga cikin kasashe na farko da suka taimakawa kasar Nijeriya wajen yaki da cutar. Ya ce, Nijeriya tana nuna godiya ga Sin da irin wannan taimako. Haka kuma, Nijeriya tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a fannonin allurar rigakafin cutar COVID-19, da horar da likitoci, da aikin noma, da makamashi da sauransu, don inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)