logo

HAUSA

Shugabannin ‘yan kasuwa na Afirka sun yi alkawarin inganta zuba jari ba tare da gurbata muhalli ba

2021-04-15 10:26:40 cri

A jiya ne, shugabannin sassan masu zaman kansa dake yankin gabashin Afirka, suka bayyana kudurinsu na goyon bayan zuba jari da zai bunkasa kiyaye muhalli da samun ci gaba tare, a wani mataki na kare mazauna yankuna daga tasirin sauyin yanayi.

Sama da jagororin ‘yan kasuwa, da jami’an diflomasiya da masana 150, wadanda suka halarci taron tattaunawa na EU da Afirka game da kare muhalli da ya gudana ta kafar bidiyo a birnin Nairobin Kenya, sun bayyana cewa, amfani da jarin masana’antu, zai taimaka matuka wajen hanzarta rage fitar da hayakin dake gurbata muhalli a yankin.

Babban sakataren kungiyar raya yankin gabashin Afirka(EAC) dake tafe Peter Mathuki, ya bayyana cewa, matakan zuba jari na baya-bayan nan a sassan yankin gabashin Afirka, sun samarwa miliyoyin mutane hanyoyin samun ruwan sha mai tsafta, da makamashin da ake iya sabuntawa, da kudade dake zama mai muhimmanci wajen inganta da kara samar da makoma mai dorewa a nan gaba.

Bankin zuba jari na Turai da ofishin jakadancin kasar Portugal dake Kenya ne, suka shiryawa shuganannin ‘yan kasuwar taron tattaunawa game da kiyaye muhalli na birnin Nairobin, gabanin dandalin manyan shugabanni game da zuba jari ba tare da gurbata muhalli ba, da zai gudana a ranar 23 ga watan Afrilu a birnin Lisbon, babban birnin kasar Portugal.(Ibrahim)