logo

HAUSA

MDD: Tashin hankalin yankin Tigray na kasar Habasha ya hana damar shigar da kayan agaji

2021-04-15 11:00:50 CRI

MDD: Tashin hankalin yankin Tigray na kasar Habasha ya hana damar shigar da kayan agaji_fororder_210415-Habasha

Hukumar samar da tallafin jinkai ta MDD ta ce, yakin da ake fama da shi a yankin Tigray na kasar Habasha ya haifar da cikas wajen hana damar shigar da kayan tallafi duk da irin damar da ake da shi na shiga yankunan.

Ofishin hukumar samar da agajin ta MDD, OCHA ta fidda sanarwa cewa, duk da kasancewar an samu ingantuwar damar shiga yankin, to sai dai ana ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula a wasu yankuna, lamarin da ya hana damar kai kayayyakin tallafin jin kai.

Lamari yana kara tsananta game da yawaitar mutanen dake tserewa daga gidajensu, ga kuma matsalolin rashin damar shiga yankunan, har yanzu ba a hakikance adadin mutanen da rikicin ya daidaita ba. A cewar alkaluman da hukumomi suka fitar an kiyasta mutane miliyan 1.7 ne suka kauracewa gidajensu a shiyyar daga ranar 27 ga watan Maris, a cewar hukumar OCHA.

Ana ci gaba da fuskantar barkewar rikici a yankunan arewa maso yammaci, da tsakiya, da gabashi, da kudu maso gabashi, da kuma kudancin shiyyar arewa maso yammacin kasar Habasha, yayin da hanyar Alamata-Mekelle-Adigrat-Shire ita ce kadai ake iya shiga a halin yanzu, in ji sanarwar OCHA.

A cewar OCHA, duk da kalubalolin da ake fuskanta, hukumomin ba da agajin suna ci gaba da yin bakin kokarinsu. A kalla mutane miliyan 1.4 sun samu damar karbar tallafin abinci har karo biyu a wasu gundumomi 12 da garuruwan Mekelle da Shire. An samarwa sabbin mutane 160,000 da rikicin ya daidaita wuraren zama da muhimman kayayyakin tallafin bukatu. A yanzu haka, sama da mutane 630,000 suna samun damar amfani da ruwa mai tsafta karkashin shirin samar da ruwan sha. (Ahmad)