logo

HAUSA

Kasar Somaliya ta fara yiwa ‘yan kasarta alluran riga kafin Sinopharm na kasar Sin

2021-04-15 09:48:19 cri

Ma’aikatar lafiya ta kasar Somaliya a jiya Laraba ta fara yiwa ‘yan kasarsa alluran riga kafin Sinopharm na kasar Sin, a wani mataki na bunkasa yaki da annobar COVID-19 a kasar dake yankin kahon Afirka.

Mataimakin ministan lafiya na kasar Ahmed Hussein, ya karbi riga kafinsa na farko na kamfanin Sinopharm, lokacin da aka kaddamar da shirin a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar. Shirin da ma’aikatar ta ce, za ta ba da muhimmanci ga ma’aikatan lafiya dake aikin yaki da annobar, da masu samar da hidimomi na musamman da kuma tsofaffi.

A jawabinsa bayan karbar riga kafin, mataimakin ministan ya bayyana cewa, kasarsa tana godiya ga kasar Sin bisa goyon baya da ta ba ta a yakin da take yi da annobar COVID-19 a kasar.

Shirin riga kafin da aka kaddamar a wani asibiti dake birnin Mogadishu, yana zuwa ne bayan da a ranar 11 ga watan Afrilu, kasar ta Somaliya ta karbi wani kaso na alluran riga kafin kamfanin Sinopharm na kasar Sin. A ranar 16 ga watan Maris din da ya gabata ne dai, kasar dake yankin kahon Afirka ta kaddamar da shirin yiwa ‘yan kasar alluran riga kafin annobar COVID-19, bayan karbar alluran karkashin shirin nan na COVAX. (Ibrahim)