logo

HAUSA

Kome nisan dare gari zai waye

2021-04-15 13:34:47 CRI

Kome nisan dare gari zai waye_fororder_1

Masu iya magana na cewa, gaskiya ba ta buya, ko min nisan dare, gari zai waye. Wannan karin magana ya dace da batun jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Ta yaya wasu ‘yan siyasar kasar Amurka da na yammacin duniya suka kitsa karairayi kan batun Xinjiang? Kwanan nan ne wani rahoto na musamman da aka wallafa a tashar intanet ta jam’iyyar Australian Citizens ya bada amsa kan wannan batu.

Rahoton mai shafi 40, mai taken “Xinjiang: Yankin yammacin kasar Sin dake tsakiyar Turai da Asiya”, ya tona asirin Amurka da Birtaniya da wasu kasashen yammacin duniya, na nuna goyon-baya ga ‘yan a-ware da masu aikata ayyukan ta’addanci da zummar cimma muradun siyasa, da illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sin, tare kuma da kawo tsaiko ga ci gabanta.

Rahoton ya ce, tun a shekara ta 2003, hukumar leken asirin Amurka wato CIA ta bada shawara cewa, lokacin da kasar take fuskantar rikici ko yin fito-na-fito da kasar Sin, za ta iya amfani da batun da ya shafi jihar Xinjiang don matsawa kasar Sin lamba. Tun shekara ta 2004 zuwa yanzu, gidauniyar dake rajin wanzar da demokiradiyya mai suna the national endowment for democracy ta Amurka ta samar da tallafin dala miliyan 8.76 ga masu yunkurin raba Xinjiang daga kasar Sin dake kasashen waje, don nuna adawa da manufofin gwamnatin kasar kan jihar Xinjiang. Har wa yau, a watan Nuwambar shekara ta 2020, ‘yan siyasar Amurka sun cire kungiyar East Turkestan Islamic Movement, wadda kasashen duniya suka ayyana ta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, daga jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda, a wani yunkuri na marawa ‘yan ta’addan baya.

Bugu da kari, duba da yadda kwalliya ta biya kudin sabulu ga gwamnatin kasar Sin a fannin daukar matakan yaki da ayyukan ta’addanci, masu kyamar kasar Sin daga kasashen Amurka da Birtaniya sun yi fushi har sun kulla makarkashiya tare da wasu cibiyoyi don kitsa karairayi masu tarin yawa dangane da jihar Xinjiang a matsayin wai shaidu, da kuma hayar wasu kafofin watsa labaransu don yada rahotanni, da nufin jirkita gaskiya da shafawa gwamnatin kasar Sin bakin fenti.

Kome nisan dare gari zai waye_fororder_2

Rahoton nan ya kuma tona asirin wadannan mutane, tare da wallafa sunayen wasu cibiyoyi ko kungiyoyin da suke yunkurin yada jita-jita game da Xinjiang, ciki har da kungiyar Amnesty International dake Birtaniya, da kungiyar Human Rights Watch ta Amurka, da cibiyar nazarin manyan tsare-tsare da manufofi ta Australiya wato ASPI da sauransu.

Kwanan nan ne, cibiyar ASPI ta bayyana cewa, wai an sake gina dimbin cibiyoyin da ake tsare mutane a sassa daban-daban a jihar Xinjiang, amma hakikanin gaskiya ita ce, kaso 90 bisa dari na hotunan wuraren da ta wallafa, ma’aikatu da asibitoci da gidaje da shaguna ne.

A kasashen yammacin duniya, makircin da wasu masu adawa da kasar Sin suka kulla a bayyana ne yake. Kwanan nan ne kuma, aka wallafa wani hoton bidiyon da tsohuwar mai tafinta daga hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka wato FBI, Sibel Edmonds ta shirya game da jihar Xinjiang, inda ba tare da wata rufa-rufa ba, ta furta cewa, Amurka na shirin yin amfani da dabarunta iri daya da wadanda suka shafi kasashen Afghanistan da Ukraine da Iraki a kan jihar Xinjiang ta kasar Sin, wato kirkiro karairayi da yada su. Amma duk da haka, Sibel Edmonds ta bayyana a shirin bidiyon cewa, bayanin da kasar Sin ta yi ya fi kama da gaskiya fiye da kalaman kasashen yamma.

To, menene gaskiyar bayanan? Gani ya kori ji, in ji malam Bahaushe.

Kwanan nan ne, wani shahararren mai hada gajerun shirin bidiyo daga kasar Isra’ila, Raz Galor ya yi tattaki zuwa gundumar Shaya dake yankin Aksu na jihar Xinjiang, inda ya ganewa idanunsa yadda ake noman auduga ta hanyar zamani. Yayin da yake zantawa da kafar CMG, ya ce, abun da ya fi burge shi a ziyararsa jihar Xinjiang shi ne, kome lafiya kalau a wajen, kana, kowa na aiki tukuru don samun rayuwa mai dadi.

Har wa yau, wani dan asalin kasar Birtaniya wanda ya dade yana zaune a kasar Sin, Jason Lightfoot, ya wallafa wani bidiyo kwanan baya, inda ya tona asirin wasu kafafen yada labaran kasashen yamma na jirkita gaskiya, da kirkiro labaran bogi da nufin kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sin.

Babu shakka, ana kara samun kasashen dake nuna goyon-baya ga kasar Sin kan batun jihar Xinjiang, al’amarin da zai karyata jita-jitar da kasashen yammacin duniya suke yunkurin yadawa.(Murtala Zhang)