logo

HAUSA

Ra’ayin Xi Jinping game da tsaron kasa

2021-04-15 17:00:44 CRI

Ra’ayin Xi Jinping game da tsaron kasa_fororder_tsaro-1

Tsaro shi ne tushen ci gaban kowace kasa. Idan babu tsaro, ba za a iya raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a ba. Ganin haka ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora muhimmanci kan aikin tabbatar da tsaro matuka, inda ya sha nanata cewa, aikin tsaro ya shafi bangarori daban daban na kasa, gami da fannoni daban daban na harkokinta, dole ne a yi kandagarkin hadarin da ka iya kunno kai, yayin da ake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ra’ayin Xi Jinping game da tsaron kasa_fororder_tsaro-3

Ya ce, dole ne a tabbatar da jagoranci mai kyau don tabbatar da tsaro a wasu muhimman fannoni da sana’o’i na kasa. Da gudanar da hadin gwiwa tare da sauran kasashe, maimakon ci gaba da yakin cacar baki. Kana dole ne a bi hanyar raya kasa cikin lumana.

Ra’ayin Xi Jinping game da tsaron kasa_fororder_tsaro-4  Ra’ayin Xi Jinping game da tsaron kasa_fororder_tsaro-2

Wadannan bayanai na daga cikin ra’ayin shugaban kasar Sin Xi Jinping game da aikin tsaron kasa. Mene ne ra’ayoyinku dangane da kalaman nasa? Ya kamata dukkanmu mu yi kokarin ba da gudunmawa ga aikin tabbatar da tsaro a kasashenmu, gami da zaman lafiya a fadin duniya. (Bello Wang)

Bello