logo

HAUSA

Kasashen Sin da Koriya ta kudu sun bukaci Japan da ta kula da batun ruwan dagwalon nukiliyar da take son zubarwa a teku yadda ya kamata

2021-04-15 11:07:13 cri

Kasashen Sin da Koriya ta kudu, a jiya Laraba sun bukaci kasar Japan, da ta dai-dai batun ruwan dagwalon tashar nukiliyar nan ta Fukishima da take kokarin zubarwa a cikin teku, ta hanyar cikakkiyar tattaunawa da hukumomin kasa da kasa da kasashe makwabtanta, da ma sauran kasashen da abin ya shafa.

Wannan kira na zuwa ne, yayin wani taron tattaunawa da matakan hadin gwiwa irinsa na farko, kan harkokin da suka shafi teku da kasashen biyu suka kira ta kafar bidiyo.

Kasashen Sin da Koriya ta kudu, sun bayyana rashin amincewarsu karara, game da shawarar da Japan ta yanke, na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku, duk da adawar da kasashen duniya, musamman Sin da Koriya ta kudun, a matsayinsu na manyan kasashe makwabtanta suka nuna.

Sin da Koriya ta kudu din, duk sun yi alkawarin sanya ido kan wannan batu. Sun kuma bayyana kudirinsu na yin aiki da ragowar kasashen duniya da ma kasashen dake shiyyar, wajen ganin sun dauki matakan da suka dace, don mayar da martani kan wannan kalubale da duniya ke fuskanta.

A ranar Talatar da ta gabata ce, kasar Japan ta sanar da shawarar da ta yanke, ta zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliyar Fukushima a cikin teku. Japan dai ta tara ruwa mai tururin guba mai yawan gaske, tun bayan hadarin tashar nukiliyar da ta faru a shekarar 2011, sakamakon girgizar kasa da igiyar ruwa ta tsunami.(Ibrahim)