logo

HAUSA

Shugaban Afghanistan Ghani ya ce ya yi maraba da matakin Amurkar na janye dakarunta

2021-04-15 11:21:34 CRI

Shugaban Afghanistan Ghani ya ce ya yi maraba da matakin Amurkar na janye dakarunta_fororder_210415-sojojn Amurka

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani, ya ce ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta wayar tarho game da matakin da Washington ta dauka na janye dukkan dakarun Amurkar daga kasarsa ya zuwa ranar 11 ga watan Satumba. Ashraf Ghani ya ce, jamhuriyar musulunci ta Afghanistan tana martaba matakin da Amurkar ta dauka kuma za su yi aiki tare domin samun nasarar janye dakarun Amurkan daga kasar, kamar yadda shugaba Ghani ya bayyana a shafinsa na Twitter.

A ranar Laraba, ita ma kungiyar tsaro ta (NATO) ta amince da janye dukkan dakarun kawancenta daga kasar Afghanistan bayan da Amurka ta sanar cewa dukkan sojojinta za su fice daga kasar zuwa ranar 11 ga watan Satumba.

Bisa la’akari da cewa babu bukatar amfani da sojoji a matsayin hanyar magance kalubalolin tsaro da kasar Afghanistan ke fuskanta, kungiyar tsaro ta NATO ta yanke kudirin fara janye dakarunta tun daga ranar 1 ga watan Mayu kuma za ta kammala cikin watanni kalilan, kamar yadda sanarwar da ministocin harkokin waje da na tsaro na kasashen mambobin kungiyar NATO suka fitar a taronsu ta kafar bidiyo wanda suka gudanar a ranar Laraba. A cewar sanarwar, duk wani harin da aka kaddamar kan mayakan Taliban daga dakarun kawancen a lokacin wannan janyewar ficewar zai fuskanci martani mai zafi. Janye dakarun kawancen ba yana nufin kawo karshen dangantakar dake tsakanin NATO da Afghanistan ba ne. Sai dai ma, hakan tamkar bude wani sabon shafi ne game da dangantakarsu.