logo

HAUSA

Sin za ta kara zamanantar da masana’antunta

2021-04-15 10:35:25 CRI

Sin za ta kara zamanantar da masana’antunta_fororder_210415-masanaantun zamani

Manyan kamfanonin kasar Sin da kudin shigar da suke samu a shekara ya kai yuan miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 3.06, za su koma tsarin zamani nan da shekarar 2035, kamar yadda bayanan da ma’aikatar masana’antu da fasahar zamani ta kasar ta sanar.

Sanarwar ta bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2025, wadannan kamfanoni za su cimma nasarar sauyawa zuwa tsarin zamani, yayin da manyan kamfanoni a muhimman bangarori za su cimma nasarar komawa zuwa tsarin amfani da fasahohin zamani.

A cewar sanarwar, ana sa ran za a samu muhimmiyar bunkasuwa a fannonin fasaha, da yin takara a kasuwanni, da amfani da fasahohin zamani a masana’antu, da samar da na’urorin zamani da sabbin manhajoji nan da shekarar 2025.

Sabbin injuna da na’urorin masana’antu masu fasahohin zamani za su biya bukatun cikin gida da kashi 70 bisa 100, yayin da manhajojin masana’antu na zamani za su biya bukatun cikin gida da kashi 50 bisa 100 nan da shekarar 2025, a cewar bayanan da aka fitar da nufin tattaro ra’ayoyin jama’a. (Ahmad)