logo

HAUSA

An bude bikin bajen kolin Canton Fair ta kafar bidiyo

2021-04-15 14:01:35 CRI

An bude bikin bajen kolin Canton Fair ta kafar bidiyo_fororder_210415-catoon fair

A yau ne, aka bude bikin baje kolin shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin karo na 129, da ake kira Cantoon Fair, ta kafar bidiyo, inda aka samu karuwar kayayyakin da aka baje kolinsu a bikin na wannan karo.

Mai magana da yawun bikin baje kolin Xu Bing, shi ne ya bayyana haka, yana mai cewa, kamfanonin dake halartar bikin, sun baje kolin sama da kayayyaki miliyan 2.7, fiye da kayayyaki dubu 230 kan na bikin da ya gabata.

Xu ya bayyana cewa, bikin na bana, ya tanadi rumfunan baje koli kimanin 60,000, inda masu baje koli na cikin gida da kasashen waje 26,000 za su baje hajojinsu. Fadin sashen kayayyakin da ake shigo da su bai sauya ba, inda ake sa ran zai dauki kamfanoni 340 daga kasashe da yankuna 28 na duniya.

Wannan shi ne karo na uku, da ake gudanar da bikin ta kafar bidiyo, bayan wadanda suka gudana a watannin Yuni da na Oktoban shekarar da ta gabata.

Haka kuma yayin bikin na bana, za a baje kolin sabbin kayayyaki 820,000, fiye da kimanin 90,000 kan na bikin da ya gabata. Masu shirya bikin baje kolin za su gabatar da sabbin kayayyaki 137 da manyan kamfanoni 85 suka gabatar ta hanyar hotuna da bidiyo da 3D, da fasahar VR.

A ranar 24 ga watan Afrilu ne, ake saran za a rufe bikin baje kolin da za a shafe kwanaki gona ana yin sa. (Ibrahim)