logo

HAUSA

Kasar Iran tana shirin fara tace kaso 60 cikin 100 na sinadarin Uranium

2021-04-14 11:03:40 CRI

Kasar Iran tana shirin fara tace kaso 60 cikin 100 na sinadarin Uranium_fororder_210414-Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, ya ce kasarsa ta sanar da hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa, shirinta na fara tace kaso 60 cikin 100 na sinadarin Uranium, biyo bayan harin da aka kaiwa tashar nukiliyarta dake Natanz.

Gidan talabijin din kasar ta Iran ya ruwaito Araqchi na cewa, nan ba dadewa ba, Iran za ta gyara sassan tashar ta Natanz da suka lalace sakamakon harin.

Haka kuma jagoran na Iran a tattaunawar shiga tsakani da ta gudana a birnin Vienna da wakilan kasashen Burtaniya da Sin da Faransa da Rasha da Jamus ya bayyana cewa, Iran za ta kara kafa wasu na’urori guda 1,000, wadanda ke da karfin tace kaso 50 na sinadarin na Uranium.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai, tashar tace sinadarin uranium ta Natanza ta fuskanci wani hadari, da mahukuntan Iran suke zargin Isra’ila da kaiwa da nufin yiwa shirinta na nukiliya zagon kasa. (Ibrahim Yaya)