logo

HAUSA

An sake zaben Patrice Talon a matsayin shugaban Benin

2021-04-14 09:50:02 CRI

An sake zaben Patrice Talon a matsayin shugaban Benin_fororder_210414-Benin

Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa, kwarya-kwayar sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (ANEC) ta fitar, ya nuna cewa, shugaan kasar mai ci Patrice Talon da mataimakinsa Chabi Talata, sun lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata, da kaso 86.37 cikin 100 na kuri’un da aka kada. Amma, sai kotun kundin tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sakamakon wucin gadin.

A shekarar 2016 ne dai, aka zabi Patrice Talon a matsayin shugaban kasar ta Benin. Kana a farkon wannan shekara, ya sanar da aniyarsa ta sake neman wa’adi na biyu na shekaru biyar a hukumance.

Bisa tanade-tanaden sabuwar dokar zaben kasar ta Benin, ana zaben shugaba da mataimakinsa kan wannan mukami ne, ta hanyar lashe kuri’un ’yan kasa da suka cancanci yin zabe suka kada, inda za su yi wa’adin shekaru biyar, za kuma a sake zabensu sau daya kacal. (Ibrahim)