logo

HAUSA

Xi Jinping ya karbi takardun kama aikin sabbin jakadun kasashen ketare

2021-04-14 20:25:43 CRI

Xi Jinping ya karbi takardun kama aikin sabbin jakadun kasashen ketare_fororder_习近平

A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amshi takardun kama aikin sabbin jakadun wasu kasashen ketare 29. Jakadun sun hada da na Afirka ta kudu, da Gambia, da kuma na Guinea-Bissau.

Da yake karbar jakadun, shugaba Xi ya jaddada cewa, har kullum al’ummar Sinawa na martaba kawance, da kauna, da zaman lafiya, kuma a shirye suke su kara zurfafa abota, da amincewa da juna, da fadada hadin gwiwa da al’ummun sauran kasashen duniya, karkashin manufar daidaito da cin moriyar juna. Daga nan sai ya yi fatan jakadun, za su ba da muhimmiyar gudummawa wajen raya dangantakar kasashen su da kasar Sin. (Saminu)