logo

HAUSA

Sin za ta kera manyan kugiyoyin tura jiragen ruwa guda 5 a tekun Suez Canal na kasar Masar

2021-04-14 11:18:04 CRI

Sin za ta kera manyan kugiyoyin tura jiragen ruwa guda 5 a tekun Suez Canal na kasar Masar_fororder_210414-Masar

Hukumar kula da tekun Suez Canal ta kasar Masar (SCA), ta kulla yarjejeniya da kamfanin kera jiragen ruwa na kasar Sin domin gudanar da aikin kera wasu manyan kugiyoyin tura jiragen ruwa guda 5 kuma a nan gaba ake sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar SCA, Osama Rabie, ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Rabie ya ce, sun riga sun cimma matsaya da kamfanin kasar Sin cewa za a kammala aikin kera jirgin ruwan na farko kuma a mika su ga kasar Masar cikin watanni 14, na biyu za a kammala shi cikin watanni 20, kana za a kammala aikin kera dukkan manyan kugiyoyin tura jiragen ruwa cikin shekaru 3 masu zuwa. Rabie ya bayyana hakan ne a bayan kammala bikin murnar zuwan babban jirgin aikin yashe teku wanda aka gudanar a yankin arewa maso gabashin lardin Ismailia.

Rabie ya kara da cewa, za su hada kai da kasar Sin domin samun nasarar aikin kera wadannan katafaren kugiyoyin tura jiragen ruwa, sannan ya bayyana kwarin gwiwa game da hadin gwiwar dake tsakanin hukumar SCA da kasar Sin.

A nasa bangaren, Mostafa Kenawy, shugaban sashen aikin yashe teku na hukumar SCA, ya bayyana cewa, baya ga aikin kera manyan kugiyoyin tura jiragen ruwa guda biyar wanda kasar Sin za ta gudanar, kana galibin sassan jiragen da hukumar SCA za ta samar sun kasance kirar kasar Sin ne. (Ahmad)