logo

HAUSA

Hada hadar shigowa da fitar da hajoji da mizanin su na Sin sun bunkasa a rubu’in farko na bana

2021-04-14 20:53:12 CRI

Hada hadar shigowa da fitar da hajoji da mizanin su na Sin sun bunkasa a rubu’in farko na bana_fororder_外贸-2

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce a rubu’in farko na shekarar bana, daukacin hada hadar shigowa, da fitar da hajoji na kasar Sin sun yi kyakkyawar bunkasuwa. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa, Sin ta samu babban ci gaba a harkokin cinikayar waje.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, darajar hajojin da kasar ta shigo da su, da wadanda ta fitar ta karu da kaso 29.2%, sama da na shekarar bara.

Da yake tsokaci game da hakan, daraktan sashen cinikayyar waje a ma’aikatar Li Xingqian, ya ce dukkanin alkaluman sun kai matsayin koli a wannan wa’adi.

Li Xinggan ya kara da cewa, “Kyawun da hada hadar cinikayyar waje ta Sin ta yi a rubu’in farko na bana, ba wai sakamakon hadin gwiwar gwamnati, da masana’antu da kamfanoni ne kadai ba, domin kuwa hakan na da nasaba ma da karfin gwiwar da masu sayayya na kasa da kasa ke da shi ga fannin cinikayyar waje na Sin.”

Ya ce a halin yanzu, ba a kai ga dakile yaduwar annobar COVID-19 a sassan duniya daban daban ba, kuma tattalin arzikin kasa da kasa, da yanayin cinikayya yana da matukar sarkakiya yana kuma sauyawa. Don haka Li Xingqian ya ce, Sin na maida hankali matuka ga raya fannin cinikayyar waje a wannan shekara ta bana, ta yadda hakan zai ingiza, tare da tallafawa sassan dake da nasaba da hakan, da kuma wanzar da daidaito, da gudanar da ayyukan masana’antu, da samar da hajoji yadda ya kamata.  (Saminu)