logo

HAUSA

Sama da yara ’yan makaranta 20 gobara ta hallaka a jamhuriyar Nijer

2021-04-14 10:09:43 CRI

Sama da yara ’yan makaranta 20 gobara ta hallaka a jamhuriyar Nijer_fororder_210414-Niger

Hukumar kashe gobara a Yamai ta sanar cewa, sama da kananan yara dalibai 20 ne suka mutu da yammacin ranar Talata a sanadiyyar tashin gobara a wata makarantar dake kwaryar birnin Yamai a jamhuriyar Nijer.

A cewar kwamandan hukumar kashe gobarar dake Yamai, Konel Sidi Mohamed, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 4 na yamma daga bisani wutar ta fantsama cikin sauri zuwa dukkan ajujuwan daliban wadanda aka gina da ciyayi, inda daliban suka makale a ciki.

Firaministan Nijer Ouhoumoudou Mahamadou, tare da rakiyar ministocin ilmi da harkokin cikin gidan kasar, sun ziyarci wajen da iftila’in ya faru tare da bayyana ta’aziyya a madadin su kansu da gwamnatin kasar ga iyalan daliban da lamarin ya ritsa da su.

Ya ce, wannan hakikanin abin bakin ciki ne, kana ya ce za su gudanar da bincike kuma muddin aka gano wasu ne ke da hannu wajen faruwar lamarin za a hukunta su. (Ahmad)