logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Manyan Tafkuna

2021-04-13 09:59:43 CRI

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Dai Bing, ya yi kira da a yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Manyan Tafkuna, ta hanyar ci gaba da dorawa kan kokarin da ake yi a yanzu.

Dai Bing ya ce an shafe wani lokaci kasashen yankin na jajircewa wajen shawo kan tasirin COVID-19, da zurfafa hadin gwiwa da aminci da inganta ci gaba na bai daya, wanda ya samar da wani yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce a lokaci guda kuma, yankin na fama da rikicin masu dauke da makamai da rikicin kabilanci tare da ci gaba da fuskantar tarin kalubalen tattalin arziki da zaman takewa da na yanayin rayuwa, abun da ke bukatar kasa da kasa su kara mayar da hankali a kai tare da zuba jari.

Dai Bing ya kuma yi kira da a jajirce wajen aiwatar da tsarin zaman lafiya da tsaro da hadin gwiwa ga Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a yankin.

A cewarsa, a baya bayan nan, kalubalen tsaro dake aukuwa kan iyakoki a yankin, sun ragu sosai. Kuma kasashe da dama a yankin sun kammala manyan zabukansu. Bugu da kari, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na ci gaba da kyautata hulda da kasashe makwabta. Kana an dawo da tattaunawa tsakanin Burundi da Rwanda. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha