logo

HAUSA

Japan ta yanke kudurin mayar da gurbataccen ruwan Fukushima cikin teku duk da adawar da take fuskanta a ciki da wajen kasar

2021-04-13 11:12:15 CRI

Japan ta yanke kudurin mayar da gurbataccen ruwan Fukushima cikin teku duk da adawar da take fuskanta a ciki da wajen kasar_fororder_210413-Japan

Firaministan Japan Yoshihide Suga ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yanke shawarar shigar da gurbataccen ruwan cibiyar makamashinta dake Fukushima zuwa cikin teku duk da adawar da take fuskanta a cikin gidan kasar da kuma kasa da kasa.

Suga ya sanar da matakin ne bayan kammala taron ganawa da ministocin da lamarin ya shafa domin tsara yadda za a mayar da dagwalon ruwan cibiyar makamashin nukiliyar kasar mai cike da sinadarai zuwa tekun Pacific.

Tashar nukiliyar wacce ta gamu da mummunar girgizar kasa mai karfin kasa da maki 9.0 wacce ta haifar da bala’in ambaliyar ruwan tsunami wanda ya girgiza shiyyar arewa maso gabashin kasar Japan a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2011, kusan kashi 1 bisa 3 na na’urorin tashar nukiliyar Fukushima Daiichi ya fuskanci mummunanr durkushewa.

Shirin yana matukar fuskantar adawa mai karfi daga kamfanonin kamun kifi na Japan da kuma al’ummar kasar, yayin da wakilan kamfanonin   kamun kifin suka bayyana cewa za a shafe shekaru masu tarin yawa ba a iya farfado da barnar da matakin zai haifar ba. (Ahmad Fagam)