logo

HAUSA

An bukaci shugabannin Afrika su samar da nasu riga kafin COVID-19

2021-04-13 09:52:37 CRI

An bukaci shugabannin Afrika su samar da nasu riga kafin COVID-19_fororder_非洲疫苗

Darakta Janar ta kungiyar kula da cinikayya ta duniya wato WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce wajibi ne nahiyar Afrika ta dauki matakan tabbatar da samar da nata alluran riga kafi, domin annobar COVID-19 da ake fama da ita a yanzu da wadanda ka iya zuwa a nan gaba.

Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana haka ne yayin wani taro da aka yi ta kafar bidiyo, kan samar da riga kafi a nahiyar Afrika.

Yayin taron, shugabannin nahiyar da suka hada da shugabannin kasashe da na bangarorin kasuwanci da masana kiwon lafiya, sun bayyana cewa, samar da riga kafin a nahiyar zai kai ta ga tabbatar da tsaro a fannin tattalin arziki da lafiya.

Darakta Janar din ta kuma yi bayanin cewa, idan ana son cimma burin samar da alluran riga kafi, ya kamata a kafa cibiyoyin samar da su masu nagarta a sassan nahiyar daban-daban.

Ta ce riga kafi na bukatar abubuwa da dama, kuma ba a bukatar sarrafa dukkansu a wuri guda. Tana mai cewa, za a iya samar da su a kasashe daban-daban, shi ya sa ya kamata a duba tare da kafa cibiyoyi masu nagarta a nahiyar.

A nata bangaren, babbar sakatariyar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), Vera Songwe, ta ce akwai gagarumin ci gaban tattalin arziki a kasashen dake samar da riga kafin. Inda ta ce, wannan misali ne da ya kamata nahiyar Afrika ta kwaikwaya ta hanyar samar da nata alluran riga kafi domin kaucewa dogaro da shigar da su daga ketare. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha