logo

HAUSA

Tsohon ministan kudin Girka: Jari da Sin ke zubawa a Afirka ya zamo muhimmin tallafi sama da mulkin mallaka da kasashen yamma suka yi a nahiyar

2021-04-13 20:13:26 CRI

图片默认标题_fororder_3

Tsohon ministan kudin kasar Girka Yanis Varoufakis, ya ce jarin da Sin ke zubawa a sassan nahiyar Afirka, da kuma gina kayayyakin more rayuwar jama’a da take yi a nahiyar, sun fi zamewa nahiyar alheri, sama da mulkin mallaka da Turawan yamma suka yi a nahiyar, cikin shekaru sama da shekaru 100 da suka shude.

Tsohon ministan ya yi wannan tsokaci ne a yau Talata, lokacin da yake gabatar da makala, a wani taron karawa juna sani a Massachusetts, yayin da wasu suke bayyana fargaba game da tasirin Sin a Afirka, suna masu kallon kasar a matsayin wadda kasashen nahiyar ke matukar dogaro da ita a fannin jari, da samar da ababen more rayuwa.

Game da hakan, Mr. Varoufakis ya ce, ko kadan bai dace a kwatanta jarin da Sin ke zubawa a Afirka da mulkin mallaka ba. Saboda Sin ba ta dogaro ga matakan nuna karfin tuwo, ko tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, da nufin samun wani tasiri.

Ya ce idan aka dauki kasar Habasha a matsayin misali, dole a yabawa kasar Sin, bisa tallafin da take baiwa kasashen Afirka a fannin gine ginen manyan ababen more rayuwa. (Saminu)

CRI