logo

HAUSA

Iran ta yi tir da hari kan tashar nukiliyar Natanz

2021-04-12 14:12:20 CRI

Iran ta yi tir da hari kan tashar nukiliyar Natanz_fororder_Img325007789

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, ya ruwaito shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran, na yin tir da abun da ya kira hari kan tashar bunkasa makamashin Uranium ta Natanz.

Ya ce Iran na da hakkin daukar mataki akan masu hannu cikin harin da magoya bayansu, yana mai nanata cewa, ya kamata hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta dauki mataki.

A cewar kakakin hukumar ta Iran, Behrouz Kamalvandi, an samu wani hatsari daga bangaren tsarin rarraba wutar lantarki na tashar Natanz da safiyar ranar.

Ya kara da cewa, babu wanda ya ji rauni yayin hatsarin, kuma bai haifar da gurbatar yanayi ko muhalli ba, yana mai cewa, ana binciken musabbabinsa.

A ranar Asabar ne Iran ta yi bikin ranar Fasahar Nukiliya ta kasar. Kuma yayin bikin, an zuba gas cikin na’urorin tantance sinadarai na semi-industrial centrifuges samfurin IR-6 guda 164 inda suka fara aiki a tashar Natanz, haka kuma wasu na’urorin 30 sun shiga mataki na farko na zuba musu gas a tashar. (Fa’iza Mustapha)