logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin ya fara ginin titin da zai bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa a Kenya

2021-04-12 11:35:41 CRI

Kamfanin kasar Sin ya fara ginin titin da zai bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa a Kenya_fororder_8644ebf81a4c510fdaa701e6f4fec529d52aa513

Kasar Kenya ta kaddamar da ginin titi mai kafar binciken da zata bunkasa cinikayya da tsaro tsakaninta da kasar Uganda. Idan aka kammala, kafar binciken za ta ba kayayyaki da mutanen dake zirga-zirga tsakanin kasashen damar tsayuwa daya kacal, kafin tsallake iyaka.

Sam Ojwang, babban jami’in yankin Trans Nzoia na arewa maso yammacin Kenya ne ya jagoranci bikin aza harsahin aikin, wanda bankin raya nahiyar Afrika AfDB ya samar da kudin aiwatarwa.

Jami’in ya kuma mika aikin ga kamfanin gine-gine na kasar Sin, wanda gwamnatin kasar ta ba kwangilar gudanarwa da shi.

Tuni kamfanin gine-ginen na Sin ya fara yi wa babban titin Kitale zuwa Endebess zuwa Suam, mai tsawon kilomita 45 kwaskwarima.

Aikin na kan iyakar kasar Kenya, zai kuma kunshi ofisoshin hukumomin kwastam da na kula da shige da fice da na hukumar tattara kudin shiga ta kasar.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Uganda Yoweri Museveni ne suka amince da gina kafar yayin tattaunawar da suka yi cikin shekarar 2018 a birnin Mombasa, domin inganta cinikayya da tsaro a yankin. (Fa’iza Mustapha)