logo

HAUSA

Daliban Afirka: Idan An Hada Kai, Babu Wata Matsala Da Ba Za A Iya Shawo Kanta Ba!

2021-04-12 14:43:26 cri

A yayin da ake tinkarar annobar numfashi ta COVID-19 a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin a shekarar da ta gabata, daliban kasashen waje kimanin 400 dake karatu a sashen jami'ar nazarin harkokin kasa ta kasar Sin dake Wuhan su ma sun yi yaki da cutar tare da malamai da daliban jami’ar, kusan rabin wadannan dalibai sun fito ne daga kasashen Afirka.

Ranar 8 ga watan Afrilu ne, aka cika shekara guda da kawo karshen kangiyar da aka sanya a birnin, a wannan rana an shirya taron tattaunawa na kasar Sin karo na 4 wanda cibiyar nazarin Afirka ta kasar Sin, da ofishin harkokin waje na gwamnatin lardin Hubei, da jami'ar nazarin harkokin kasa ta kasar Sin dake Wuhan suka karbi bakunci.

Daliban kasashen Afirka dake karatu a jami’o’in daban-daban a birnin Wuhan, sun ba da labarai game da yadda aka yi yaki da annobar. Masana sama da 700 da suka halarci taron a Beijing, da wasu kasashen Afirka kamar Afirka ta Kudu, Najeriya, Uganda, da Zambiya sun halarci taron ta yanar gizo, inda suka waiwayi gogewa game da yadda aka yaki cutar cikin hadin gwiwa, kuma daliban kasashen waje sun nuna yabo kan yadda kasar Sin ke sauke nauyin dake bisa wuyanta da karfin hadin kan al’ummar kasar, a yanzu sun kuma yaba tasirin alluran rigakafin kasar ta Sin.

Daliban Afirka: Idan An Hada Kai, Babu Wata Matsala Da Ba Za A Iya Shawo Kanta Ba!_fororder___172.100.100.3_temp_9500031_1_9500031_1_6012_f2c66a5f-4b74-4cf8-9b05-4c9227cc1cf9

A shekarar da ta gabata, birnin Wuhan ya danna "maballin dakatarwa" don dakile hanyar yaduwar annobar COVID-19. A wannan lokaci, Tiando S. Damien, dalibi daga kasar Benin, ya kafa kungiyar sa kai ta daliban kasa da kasa don shiga cikin ayyukan makarantarsu na ba da tabbaci ga rayuwar daliban kasashen waje a yayin tinkarar annobar. A yayin da ya waiwayi lamarin, Tiando S. Damien ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai matukar daukar nauyinta, ko dai tabbatar da samar da isassun kaya yayin yakar annobar, ko kuma samar da alluran riga kafin, kasar Sin ba ta taba daukar daliban kasashen waje a matsayin "baki" ba. Ya ce,

"Idan muna son shawo kan annoba, ba za mu yi aiki mu kadai ba. Akwai bukatar da mu hada kai tare. A yayin yaki da annobar, mun yi aiki tare da jama'ar kasar Sin. Idan muka hada kai, babu wata matsalar da ba za mu iya shawo kanta ba. "

Mamodson Zafiniaina Adore, daga kasar Madagascar, kuma memba a kungiyar sa kai ya rera wakar al’ummar Wuhan. Yana fatan bayyana fatan alheri ga Wuhan ta hanyar rera wakar. Ya ce,

“Ko da yake ni ba a kasar Sin aka haife ni ba, amma tana cikin zuciyata. Kasar Sin ita ce kasata ta biyu.”

Mamodson Zafiniaina Adore dalibi ne da ke karatun neman digiri na uku a Jami’ar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin. Ya yi shekaru 10 yana karatu a kasar Sin. Daga rashin iya magana ko kalma daya a cikin Sinanci har zuwa iya rera wakokin kasar Sin cikin yadda ya kamata, kasar Sin ta zama garin sa na biyu a cikin shekaru goma da suka gabata. Idan aka waiwayi baya a lokaci mafi tsananin da aka yi fama da annobar a bara, Mamodson Zafiniaina Adore ya ce, abun da ya fi burge shi shi ne, yadda Sinawa suka hadin kai don yaki da annobar.

Daliban Afirka: Idan An Hada Kai, Babu Wata Matsala Da Ba Za A Iya Shawo Kanta Ba!_fororder___172.100.100.3_temp_9500031_1_9500031_1_6012_be086e3a-8e59-4a68-a70e-3504c283e89f

"Lokacin da motocin da ke cike da 'ya'yan itatuwa da kayan lambu suka nufi makarantarmu daga wasu birane, na yi matukar mamaki. A mawuyacin lokaci na yakar annobar, mun samu kayayyaki da kulawa daga yankuna masu nisa. Ba makarantarmu kawai ta ba mu abinci ba, har da Sinawa da ke wajen Wuhan su ma sun damu da mu! Irin wannan kulawa ta burge ni. Duk da cewa ba mu san juna ba, amma zukatanmu suna hade. Sun taimaka mana a lokaci mafi wahala. "

Kwanan baya, Mamodson Zafiniaina Adore ya karbi alluran rigakafin na kasar Sin na farko. Yana fatan za'a yiwa mutanen garinsu riga-kafi cikin hanzari.

"Na yi matukar farin ciki da aka yi min riga kafin. Ina fatan wata rana, iyalai na, abokai na, da kuma al’ummar Madagascar su ma za a yi musu riga kafin."

Momade Mansur Mussa dan kasar Mozambique, yana sha'awar fasahar sassaka yayin da yake karatu a kasar Sin, kuma ya kammala ayyuka da yawa a karkashin jagorancin malamansa. A yayin tinkarar annobar, ya kirkiro ayyukan sassaka sama da goma, don nuna fatan alheri ga birnin Wuhan da ma kasar Sin wajen cimma nasarar yaki da annobar. Ya kuma yi kira da a karbi alluran riga kafin.

"Ku zo a yi mana allurar tare, domin mu hada kanmu wajen yaki da cutar." (Mai fassara: Bilkisu Xin)