logo

HAUSA

Amurka ba za ta soke dukkan takunkumin da ta sakawa Iran ba

2021-04-11 16:51:09 CRI

Amurka ba za ta soke dukkan takunkumin da ta sakawa Iran ba_fororder_美国

A ranar 9 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa, Amurkar ba za ta soke dukkan takunkuman da ta sakawa kasar Iran ba, kuma tana fatan Iran din za ta dauki matakin da ya dace yayin shawarwarin da sassan biyu za su yi game da maido yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka shirya ta wayar tarho cewa, Amurka ta tsaida kuduri cewa, za ta soke wasu takunkuman da ba su da nasaba da yarjejeniyar nukiliyar Iran, amma ba za ta soke dukkan takunkumin da ta sakawa Iran ba, jami’in ya kara da cewa, idan Iran ta nace kan matsayar soke dukkan takunkuman da Amurka ta saka mata tun a shekarar 2017, mai yiwuwa ne shawarwarin da za su yi zai shiga halin kaka-nika-yi.(Jamila)