logo

HAUSA

Sakamakon zabe na wucin gadi ya nuna shugaban kasar Djibouti Guelleh ya lashe zaben kasar

2021-04-11 16:52:36 CRI

Sakamakon zabe na wucin gadi ya nuna shugaban kasar Djibouti Guelleh ya lashe zaben kasar_fororder_0411-Jibouti-Ahmad-2

Bisa ga kwarya-kwaryar sakamakon zaben da aka fitar a jiya Asabar ya nuna cewa, shugaban kasar Djibouti dake kan mulki Ismail Omar Guelleh, shi ne ya lashe zaben shugaban kasar.

Ministan al’amurran cikin gidan kasar Moumin Ahmed Cheick, ya bayyanawa kafafen yada labaran kasar cewa, sakamakon zaben na wucin gadi ya nuna shugaba Guelleh ya lashe zaben da kashi 98 bisa 100 na kuri’un da aka kada.

Tun a ranar Juma’a ne masu zabe a kasar suka jefa kuri’unsu daga safiya har zuwa karfe 7:00 na yammaci agogon kasar, daga bisani an cigaba da kirga kuri’un. Sai dai kotun tsarin mulkin kasar ce ke da ikon tabbatar sakamakon zaben nan da wasu kwanaki masu zuwa.(Ahmad)

Ahmad