logo

HAUSA

WHO: kasa da kaso 2 na wadanda aka yi wa riga kafin COVID-19 Afrika ta dauka

2021-04-10 15:49:08 CRI

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kasa da kaso 2 na jimilar riga kafi miliyan 690 da aka yi amfani da su a duniya ne Afrika ta dauka.

Daraktar hukumar a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti ce ta bayyana haka, inda ta ce duk da ci gaban da ake samu, kasashen nahiyar da dama ba su zarce matakin fara bada riga kafin ba.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya a Nairobin Kenya, daraktar ta ce karancin riga kafin ka iya kawo tsaiko ga kokarin da ake yi na dakile annobar a nahiyar, yayin da ake fuskantar barazanar barkewarta a zagaye na 3.

Ta ce matsalar karanci da samar da riga kafin, na hana mutane damar samu a nahiyar, inda ta ce idan har ana son dakile cutar, to wajibi ne a tabbatar da samar da riga kafin cikin adalci.

Kididdiga daga WHO ta nuna cewa, kasashen Afrika 45 sun riga sun karbi riga kafin, kuma 43 daga cikinsu, sun fara bayar da allurar ga rukunonin mutane mafi fuskantar barazanar kamuwa da cutar, yayin da aka yi amfani da kusan allurai miliyan 13 daga cikin miliyan 31.6 da suka riga suka isa nahiyar.

Bugu da kari, ta ce samar da riga kafin ga nahiyar bai gudana a yanayi na bai daya ba, bisa la’akari da cewa kasashe 10 sun karbi kaso 93 na alluran. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha