logo

HAUSA

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

2021-04-10 16:56:25 CRI

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa_fororder_新疆

Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto Bradanini ya ce takunkuman da kasashen Amurka da Birtaniya suka kakabawa kasar Sin a baya-bayan nan, sun keta dokokin kasa da kasa.

Yayin zantawar da ya yi jiya da kafar yada labarai ta La Lighthouse ta Italiya, tsohon jakadan ya ce takunkuman ba su bi ta hannun tsarin Kwamitin Sulhu na MDD ba, wato kasashen sun yi gaban kansu ne wajen sanya takunkuman, yana mai cewa, wannan wata hanya ce da Amurka ta dauka domin kaddamar da yakin cacar baka kan Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.

Alberto Bradanini ya ce galibin zarge-zarge game da Xinjiang dake yawo a yammacin duniya, ba gaskiya ba ne, inda ya ce akwai adadi mai yawa na wuraren ibada a Xinjiang, ciki har da Masallatai da Mujami’u da wuraren ibada na addinin Buddha da na Taosit. Ya kara da cewa, ‘yancin bin addini ya dogara ne da wasu ginshikai, kuma yana bukatar kasancewa bisa yanayi na zaman lafiya da hadin kan kasa da tsaro da kwanciyar hankali.

Ha ila yau, ya bayyana cewa, batun kisan kare dangi a Xinjiang, ba shi da wani kamshin gaskiya, yana mai cewa ya kamata a yi la’akari da karuwar al’ummar kabilar Uygur daga shekarar 1978 zuwa 2018. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha