logo

HAUSA

WHO: Za A Tantance Rigakafin Sinopharm Da CoronaVac Tsakanin Ran 26 Ga watan Afrilu Zuwa Ran 3 Ga Watan Mayu

2021-04-10 16:38:15 CRI

Alluran riga kafin COVID-19 na Sinopharm da CoronaVac na kasar Sin, sun shiga mataki na karshe na nazari domin amfanin gaggawa na hukumar lafiya ta duniya, inda za a fitar da sakamako na karshe tsakanin ranar 26 ga watan nan Afrilu da ranar 3 ga watan Mayu.

A cewar daraktan hukumar mai sa ido da tabbatar da cancantar riga kafi, Rogerio Pinto de Sa Gaspar, sun kira rukunin kwararrun da zai tantance alluran a ranar 26 ga wata, inda ya ce za a tantance akalla daya daga cikin alluran.

Ya ce idan ba a kammala tantance su duka ba zuwa ranar 26 ga wata, za a shirya wani rukunin a makon ranar 3 ga watan Mayu.

Ya kara da cewa, tsakanin makonnin biyu, suna sa ran za a cimma matsaya ta karshe dangane da alluran riga kafin biyu.

Nazarin riga kafi domin amfanin gaggawa, wanda tsarin hukumar WHO ne na tantance riga kafin mara lasisi, wajibi ne ga riga kafin da za a yi amfani da shi karkashin shirin COVAX, wanda ke da nufin samar da riga kafi cikin adalci ga kasashen masu karanci da matsakaicin kudin shiga. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha