logo

HAUSA

Ecuador ta karbi kashin farko na riga kafin kamfanin Sinovac na kasar Sin

2021-04-09 13:15:00 xri

Kasar Ecuador ta karbi kashin farko na alluran rigakafin kamfanin Sinovac na kasar Sin a jiya, da nufin yaki da annobar COVID-19.

Shugaban kasar Lenin Moreno ne ya tarbi riga kafin, tare da ministan harkokin wajen kasar, Manuel Mejia da jakadan Sin dake kasar, Chen Guoyou.

A cewar Jakada Chen, ranar ta musammam ce, kuma mai muhimmanci ga dangantakar kasashen biyu, da hadin gwiwarsu a yaki da annobar da kokarin kasar na yi wa al’ummarta riga kafi.

Ya kara da cewa, tun bayan barkewar annobar, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar wasiku da sakonni a tsakaninsu, haka kuma sun zanta ta wayar tarho da zummar nuna goyon bayansu ga juna a yaki da annobar.

Har ila yau, ya ce dangantakar kasashen biyu ya samu nasararori tare da kara karfi yayin da ake fuskantar annobar, inda Sin ta taimakawa Ecuador da kayayyakin kiwon lafiya kamar motocin daukar mara lafiya da na’urar taimakon numfashi da makarin baki da hanci. (Fa’iza Mustapha)