Yanayin kare hakkin dan-Adam a Amurka
2021-04-09 20:00:08 CRI
Amurka ce ke da sama da kaso 25 cikin 100 na wadanda da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duniya, inda cutar ta halaka Amurkawa sama da dubu 550, kusan kaso 20 cikin 100 na yawan wadanda cutar ta halaka a duniya.
Daga shekarar 1945 zuwa 2001, an samu tashe-tashen hankula na masu dauke da makamai 248 a kasashe da yankuna 153 na duniya, kuma Amurka ce ta haddasa 201 daga cikinsu, adadin da ya kai kimanin kaso 81 cikin 100.
Maza matasa Amurkawa ‘yan asalin Afirka, suna fuskantar barazar harbi fiye da sau 21 kan takwarorinsu fararen fata daga ‘yan sandan kasar. Haka kuma yadda ake harbe maza bakaken fata ‘yan asalin Amurka ‘yan tsakanin shekaru 15 da 19 ya kai 31.17 cikin miliyan 1. (Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Sama da Amurkawa 20,000 sun harbu da sabbin nau’ikan cutar COVID-19
- Sin: Yake-Yaken Da Amurka Ta Tayar Sun Haifar Da Dimbin Matsalolin Jin Kai A Duniya
- Ikenna Emewu: Kasar Amurka tana da mugun manufar dakatar da ci gaban kasar Sin
- Jami’in Rasha: Tabbas Ana Kera Makamai Masu Guba A Dakin Gwaje-gwajen Amurka Dake Kusa Da Kan Iyakar Rasha Da Kasar Sin