logo

HAUSA

Sin: Yake-Yaken Da Amurka Ta Tayar Sun Haifar Da Dimbin Matsalolin Jin Kai A Duniya

2021-04-09 13:19:34 CRI

Kungiyar bincike hakkin bil Adama ta kasar Sin, ta ba da wani bayani a yau mai taken “Yake-yaken da Amurka ta tayar sun haifar da dimbin matsalolin jin kai masu tsanani a duniya”, inda bayanin ya fayyace cewa, Amurka na fakewa da "sa hannu domin nuna jin kai" don nuna karfin tuwo a wasu yankuna, abin da ya janyo rasa rayukan sojoji da dama, da fafaren hula, ya kuma haifar da fatara da asarar dukiyoyi, wanda ya zama wata matsalar jin kai mai tsanani sosai.

Bayanin ya nuna cewa, Amurka ta tayar da yake-yake sau 201, daga cikin 248 da suka auku a yankuna 153 na duniya, tun bayan yakin duniya na biyu zuwa shekarar 2001.

Bayanin ya kuma ce, rikicin jin kai da Amurka ta haifar, dangane da daukar matakan soja, na da alaka da tunanin babakere, kuma duk kasar dake nacewa ga wannan tunani ba za ta kula da hakkin Bil Adama na sauran kasashe ba ko kadan.

Kaza lika yin watsi da tunanin son kai, hanya ce daya tilo da za a iya amfani da ita wajen kauracewa barkewar matsalar jin kai, ta yadda za a samu cin gajiyar juna, da cin moriya tare, kuma jama’ar kasashen duniya za su tabbatar da hakkinsu. (Amina Xu)