logo

HAUSA

Ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na G20 sun yi kira da a samar da goyon baya domin farfado da tattalin arzikin duniya

2021-04-08 11:57:18 CRI

Ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na G20 sun yi kira da a samar da goyon baya domin farfado da tattalin arzikin duniya_fororder_hoto

A jiya Laraba ne aka rufe taron ministocin harkokin kudi, da shugabannin bankunan tsakiya na kungiyar G20 a birnin Roma, fadar mulkin kasar Italiya. Wannan shi ne taron ministocin harkokin kudi karo na biyu da aka fara yi, tun bayan da kasar Italiya ta karbi matsayin shugabancin kungiyar ta G20.

A yayin taron, bangarorin da abin ya shafa, sun cimma matsayi daya kan wasu batutuwan da suka hada da bukatar magance ficewar kasashe daga manufar kara bukatun al’umma na gaggawa, da inganta aikin kwaskwarima kan tsarin karbar haraji na kasa da kasa, da sauyin yanayi, da kuma neman dauwamammen ci gaba da sauransu.

Ga karin bayani daga Maryam Yang…

Bayan taron, an gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda aka bayyana cewa, bangarorin da abin ya shafa sun cimma matsayi daya, kan batun karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, da yadda za su fuskanci kalubalolin tattalin arziki cikin hadin gwiwa. A sa’i daya kuma, sun amince da samar da goyon baya a fannin sha’anin kudi, domin farfado da tattalin arzikin duniya bayan annoba.

Kamar yadda aka gudanar da taron ministocin harkokin kudi a karo na farko, an gudanar da taron na wannan karo ne shi ma ta kafar bidiyo. Kana, a lokacin taron manema labarai da aka yi bayan taron, ministan harkokin tattalin arziki da kudade na kasar Italiya Daniele Franco, ya jaddada cewa, a ganin mahalarta taron, tabbas ne, tattalin arzikin duniya zai karu, bisa kokarin da aka yi na samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, da goyon bayan sha’anin kudi, amma, ba za a tabbatar da farfadowar tattalin arziki baki daya ba.

Ya ce sakamakon janyewar wasu kasashe daga manufar kara bukatun al’umma na gaggawa, za a fuskanci kalubale a fannin raya tattalin arziki, don haka ya kamata a rage, ko kuma soke manufar sannu a hankali. A hannu guda kuma, asusun ba da lamuni na IMF na kungiyar G20, yana rokon kara masa asusun musamman mai lakabin SDR, wanda zai kunshi dallar Amurka biliyan 650, domin biyan bukatun kasa da kasa a fannin adana kudi, da samar da goyon baya wajen farfado da tattalin arzikin duniya.

Daniele Franco ya ce,“Bisa halin da muke ciki, kungiyar G20 ta sake jaddada cewa, kada a soke matakan goyon bayan sha’anin kudi cikin sauri. A hakika dai, mun sake jaddada cewa, ya dace a dauki matakai iri iri domin samar da guraben aikin yi ga al’umma, musamman ma ga wadanda suka fi fama da matsaloli a fannin zaman rayuwa, sakamakon annobar cutar numfashi ta COVID-19.”

Cikin sanarwar hadin gwiwa, an ce, babban tushen tabbatar da rayuwa, da farfado da tattalin arziki shi ne, hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Kungiyar G20 za ta ci gaba da karfafa gina tsarin kiwon lafiya, domin kare lafiyar al’umma, da raba alluran rigakafin cutar COVID-19 ga al’umma cikin sauri, kuma bisa adalci. Malam Franco ya kara da cewa, a watan Yuli na bana, babban kwamitin kungiyar G20 mai zaman kansa wanda ke da nauyin lura da harkokin kudi, kuma dandalin kasa da kasa na tunkarar barkewar annoba, zai gabatar da bayanin kandagarki da fuskantar da annobar cutar COVID-19. An kafa wannan kwamitin bisa kiran kasar Italiya, domin samar da kudade na gina tsarin kiwon lafiyar kasa da kasa.

Cikin taron ministocin harkokin kudi na kungiyar G20 karo na farko da aka yi a bana, bangarorin da abun ya shafa sun cimma matsaya daya, cewa babban aikin dake gabanmu shi ne yin kwaskwarima ga tsarin karbar haraji na kasa da kasa, inda suka bayyana cewa, kafin karshen watan Yuni na bana, za a kulla wata yarjejeniya game da rage yawan haraji na kamfanonin kasa da kasa, da manyan kamfanonin kimiyya da fasaha. Dangane da wannan batu, Malam Franco ya ce, kungiyar G20 za ta ci gaba da yin shawarwari kan yadda za a gina wani tsarin karbar haraji na zamani mai adalci.

Ya ce,“A taron ministocin harkokin kudi karo na farko da aka yi a watan Fabrairun bana, mun yi alkawari cewa, za mu kulla wata yarjejeniya a tsakiyar bana, bisa ra’ayin daya da sassa daban daban suka cimma. A taron da muka yi a yau kuma, mun cimma wasu sakamako kan hakan, sa’an nan, za mu sa kaimi ga kungiyar G20, da kungiyar hadin gwiwa da bunkasuwar tattalin arziki, da su ci gaba da warware sauran matsalolin dake gabanmu.”

Ban da haka kuma, Daniele Franco ya ce, a watan Yuli na bana, kungiyar G20 za ta kira taron koli game da batutuwan sauyin yanayi, da kare muhalli, da kuma yadda za a cimma burin neman dauwamammen ci gaba a birnin Venice na kasar Italiya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)