logo

HAUSA

IMF: An yabawa yadda Sin ke tinkarar cutar COVID-19

2021-04-08 10:54:21 CRI

IMF: An yabawa yadda Sin ke tinkarar cutar COVID-19_fororder_1

Kasar Sin ta cancanci yabo game da yadda take tinkarar yaki da annobar COVID-19, kana ta kuma taka rawar gani game da magance manyan kalubaloli, wani jami’in asusun ba da lamini na kasa da kasa IMF ya bayyana hakan.

Kafar yada labaran CNBC ta rawaito Tobias Adrian, daraktan sashen kasuwannin hada hadar kudade na hukumar IMF yana cewa, kasar Sin ta yi nasarar dakile annobar ta hanyar amfani da kwararan matakai, kuma a kan lokaci.

Adrian ya fadawa kafar yada labaran CNBC cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya koma yanayi mai kyau tun a tsakiyar shekarar da ta gabata, kuma yana sama da na ragowar dukkan kasashen duniya.

Game da manyan kalubalolin da take fuskanta, kasar Sin ta taka rawar gani yadda ya kamata wajen magance su, a cewar jami’in na IMF.(Ahmad)