logo

HAUSA

Jami’in Rasha: Tabbas Ana Kera Makamai Masu Guba A Dakin Gwaje-gwajen Amurka Dake Kusa Da Kan Iyakar Rasha Da Kasar Sin

2021-04-08 20:38:48 CRI

Sakataren hukumar tsaron kasar Rasha Nikolai Patrushev, ya bayyana yayin wata zantawa da wakilin jaridar Kommenrsant cewa, hukumarsa ta yi imanin cewa, ana kera makamai masu guba a dakin gwaje-gwaje mallakar Amurka dake kusa da kan iyakar Rasha da Sin.

Patrushev ya bayyana cewa, dakunan binciken kwayoyin halitta na kasar Amurka dake sassa daban-daban na duniya, musamman wadanda ke kusa da kan iyakar Rasha da Sin, suna bunkasa.

A don haka, jami’in na kasar Rasha ya ce, Rasha da abokan huldarta na kasar Sin, suna da tambaya a kai. Ya ce, an fada musu cewa, tashohin dake kan iyakar kasashin biyu, cibiyoyi ne na tsaftace muhalli da yaki da annoba cikin lumana, amma da alamun, sun yi kama da irin wadda ke Maryland, inda kasar ta Amurka ta shafe gwamman shekaru, tana amfani da ita wajen nazarin kwayoyin halitta da suka shafi aikin soja.(Ibrahim)

Ibrahim