logo

HAUSA

Adadin al’ummun Afirka da aka tabbatar sun harbu da COVID-19 ya haura miliyan 4.29

2021-04-08 10:13:11 CRI

Adadin al’ummun Afirka da aka tabbatar sun harbu da COVID-19 ya haura miliyan 4.29_fororder_病毒-1

Cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, ta sanar da cewa, ya zuwa tsakar ranar jiya Laraba, adadin wadanda suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar ya kai mutane 4,291,017.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka AU, ta ce adadin mutanen da cutar ta hallaka a nahiyar ya kai 114,344, yayin da mutane 3,858,461 suka warke daga cutar a duk fadin nahiyar.

Kawo yanzu, Afirka ta kudu, da Morocco, da Tunisia, da Habasha da Masar ne ke kan gaba, wajen yawan mutane da suka harbu da wannan cuta a nahiyar, kamar dai yadda cibiyar ta Africa CDC ta tabbatar.

Bisa alkaluman cibiyar, adadin wadanda suka harbu da cutar a Afirka ta kudu ya kai mutane 1,552, 853, ita ce kuma kan gaba a nahiyar. Sai kuma kasar Morocco mai mutane 499,025, da Tunisia mai 263,043.  (Saminu)